admin

Yan Jaridun Bauchi mutum 14 sun yi hatsari a bakin aiki

Tawagar ’yan jarida kimanin su 14 da suka fito daga kafafen yaɗa labarai dabam-dabam suka gamu da mummunar hatsarin mota a yayin da suke cikin tawagar Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC). Tawagar da suke tafiya a ƙarƙashin jagorancin ƙaramin Ministan Raya Yankuna, Alhaji Uba Maigari Ahmadu a yayin da suke ziyarar buɗewa da […]

Read more

Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci ma’aikatan Abuja su koma aiki

Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci ma’aikatan Abuja su koma bakin aiki bayan cimma matsaya da ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, biyo bayan taron sulhu da aka gudanar domin warware matsalolin da suka haifar da yajin aikin da ake yi. Taron ya gudana bisa jagorancin shugaban kwamitin majalisar dattawa na Abuja, Sanata Mohammed Bomoi. Sanarwar […]

Read more

NECO ta saki sakamakon jarrabawar 2025 na dalibai masu zaman kansu

Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta saki sakamakon jarrabawar dalibai masu zaman kansu na shekarar 2025. Shugaban Hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya bayyana cewa 93,425 daga cikin daliban sun zana jarrabawar harshen Ingilishi, inda kashi 78.32% (73,167) suka samu akalla Credit. Dalibai 93,330 sun zana jarrabawar Lissafi inda kashi 91.35 % (85,256) suka samu akalla […]

Read more

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke Kano

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke birnin Kano a safiyar Litinin ɗin nan. Rahotanni sun nuna cewa ’yan kasuwa da mazauna sun shiga tashin hankali matuƙa sakamakon tashin gobarar a shahararriyar kasuwar kayan abincin kwali da da ke titin Bello Road. ‎An yi asarar dukiyoyi na maƙudan kuɗaɗe a sanadiyyar gobarar ta safiyar […]

Read more