Gwamna Namadi ya jagoranci babban taron fasaha a Argentina domin bunƙasa noman alfalfa da ci gaban kiwo a Jigawa.
A ƙoƙarinsa na mayar da Jihar Jigawa cibiyar samar da ciyawar kiwo da kasuwancin noma a Najeriya, Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci wata babbar tawagar kwararru zuwa Jamhuriyar Argentina domin nazarin dabarun ci gaban noma.
Ziyarar, wadda ake gudanarwa tare da haɗin gwiwar El-Meena Farms Limited da abokan hulɗa na ƙasashen waje ciki har da Alkhorayef Group na ƙasar Saudiyya, ta mayar da hankali ne kan bunƙasa sarkar darajar alfalfa, wadda ke da matuƙar muhimmanci a ajandar sauya fasalin harkar noma ta Gwamna Namadi.
Tawagar na nazarin ingantaccen tsarin noma na duniya a lardin Córdoba na Argentina, wuri mai yanayi kusan iri ɗaya da na Arewa maso Najeriya.
Manufar ziyarar ita ce kwaikwayon tsarin “Cluster” na Argentina, wanda ke haɗa ƙananan manoma cikin cibiyar masana’antu ta zamani domin tabbatar da wadatar abincin kiwo a gida da kuma fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin Gabas ta Tsakiya.
Gwamnan tare da tawagarsa sun gudanar da cikakken bincike a gonaki da masana’antu domin samo taswira ta musamman da za ta jagoranci sauyin harkar noma a Jigawa, inda suka kai ziyara zuwa:
Biofarma S.A., wata shahararriyar kamfani a Córdoba da ke kan gaba wajen samar da abincin dabbobi, domin fahimtar ingantattun ka’idojin kiwon lafiya da ciyarwa da za su bunƙasa harkar kiwo a Jigawa.
Masana’antar Nafosa da Pellfood, inda aka yi nazari kan sabbin fasahohin nade ciyawa a manyan bale, matse ciyawa da ƙarfi, da kuma sarrafa ta zuwa pellets.
Manyan gonakin alfalfa, wake (soya) da masara, inda tawagar ta shaida ingantaccen tsarin noman zamani, yawan amfanin gona, da amfani da dabarun ban ruwa masu tanadin ruwa.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa, “Wannan ziyara ba yawon shakatawa ba ne kawai, mataki ne na asali da zai samar da ayyukan yi tare da ƙara kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR) ga jiharmu.”
Ya ƙara da cewa, “Ta hanyar ɗaukar waɗannan tsare-tsaren masana’antu na Argentina, muna tabbatar da cewa Jihar Jigawa za ta wuce noman gargajiya zuwa noma na kasuwanci mai dogaro da fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.”
Gwamnan na tare da tawagar kwararru da suka haɗa da Kwamishinan Ma’aikatar Kiwon Dabbobi, Prof.
Abdurrahman Salim Lawal, da kuma Darakta Janar na Hukumar Sauya Fasalin Noma ta Jigawa (JATA), Dr. Saifullahi Umar.
Ana sa ran ziyarar za ta ƙare da kulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da fasaha, waɗanda za su fara aiki nan take a El-Meena Farms da kuma sauran cibiyoyin noman zamani a faɗin Jihar Jigawa.