Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci ma’aikatan Abuja su koma aiki

Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci ma’aikatan Abuja su koma bakin aiki bayan cimma matsaya da ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, biyo bayan taron sulhu da aka gudanar domin warware matsalolin da suka haifar da yajin aikin da ake yi.

Taron ya gudana bisa jagorancin shugaban kwamitin majalisar dattawa na Abuja, Sanata Mohammed Bomoi.

Sanarwar da ƙungiyoyin ƙwadagon da suka haɗa da NLC da TUC suka fitar a ranar 3 ga Fabrairu ta ce an yi tattaunawa mai zurfi tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa a taron

A cewar sanarwar, “an tattauna dukkan ƙorafe-ƙorafen da mambobin haɗakar ƙungiyar ƴan ƙwadago JUAC suka gabatar tare da magance su ɗaya bayan ɗaya.

A yayin taron, Minista Wike ya tabbatar wa ƙungiyoyin ƙwadago cewa “za a gina dangantaka bisa mutunta juna da kuma ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.”

Haka kuma, an cimma matsaya cewa babu wani ma’aikaci da za a muzanta ko a hukunta sakamakon shiga yajin aikin da aka yi a baya.

Haka zalika, ɓangarorin sun amince cewa dukkan shari’o’in da suka shafi wannan batu da ke gaban Kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago ta Ƙasa za a janye su nan take.

Sakamakon haka, ƙungiyar ta umurci ma’aikatan babban birnin tarayya da su koma aiki nan take.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto