An yi jana’izar Sajan Dalet Cikin Alhini
Rundunar Sojin Nijeriya ta gudanar da jana’izar Dokin ta Sajan Dalet Danfari Akawala.
Rundunar Sojin Nijeriya ta gudanar da jana’izar Dokin ta Sajan Dalet Danfari Akawala.
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula.
’Yan bindiga sun kai hari Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta.
‘Yan bindiga sun sace aƙalla mutane 22 a wasu sabbin hare-hare a ƙauyen Kugauta da ke Kusheka da kuma Kitanda da ke Gashere a masarautar Kumana na Ƙaramar Hukumar Kauru.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP da na Reuters sun ce Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada.
Rahotanni daga Enugu Kudancin Najeriya na cewa aƙalla mutum 18 sun mutu sakamakon hatsarin wata tanka da ta yi bindiga.
Gamayyar hukumomin tsaro a jihar Kano sun gargadi mutane da su kaucewa wuraren cunkoson jama’a sakamakon samun bayanan sirri kan yunkurin kawo hare-hare jihar da wasu yan ta’adda ke shirya wa.
Ana zargin wata ɗaliba a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, da sa samarin ta su yi wa wani malaminsu mai suna Aliyu Hamza Abdullahi dukan kawo wuƙa.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce dole sojoji su mamaye dazuka domin kawo ƙarshen ’yan bindiga a Najeriya.
Shugaban Amurka na 47 Donald Trump ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya a duniya yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar yau Litinin 20 ga Janairun 2025.