Ya Kamata Sojoji Su Mamaye Dazukan Najeriya-Ganduje

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce dole sojoji su mamaye dazuka domin kawo ƙarshen ’yan bindiga a Najeriya.

Dokta Ganduje, ya bayyana haka ne, yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, kan hatsarin tankar mai da ya yi sanadin rasuwar mutane da dama a makon da ya gabata.

Da ya ke tsokaci dangane da matsalar ‘yan bindiga, Ganduje ya ce;“Maganin wannan matsala shi ne mamaye dazuka, domin nan ne ‘yan bindiga suke buya.

“Me ya sa muke kare kanmu kawai maimakon mu kai musu farmaki? Lokacin da nake Gwamnan Kano, na roƙi Gwamnatin Tarayya ta bai wa sojoji damar mamaye dajin Falgore.

“Sojojin sun kafa cibiyar horo a can, kuma hakan ya sa aka fatattaki ’yan bindiga daga dajin. Yanzu haka Kano na zaman lafiya,”

A jawabin godiyarsa ga Dokta Ganduje, Gwamnan jihar Neja Umaru Bago, ya gode wa Ganduje da shugabancin APC bisa goyon bayan da suke bai wa jihar.

Bango ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gyara manyan titunan jihar, kamar hanyar Suleja zuwa Minna, domin rage haɗura da ƙara tabbatar da tsaroa jihar Neja.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda