SNB Ta Buɗe Ofis A Jihar Kano

Daga Mujahid Wada Musa

Ƙungiyar Ma’aikatan Kafafen Yaɗa Labarai Ta Ƙasa SNB ta buɗe ofis a jihar Kano, a wani ɓangare na ci gaba da taron bitar kara wa juna sani na kwanaki biyu da tsangayar koyar da aikin Jarida ta jami’ar Bayero Kano tare da haɗin gwiwar ƙungiyar SNB suka shirya.

Da yake bude Sabon ofishin, shugaban ƙungiyar na kasa Farfesa Umaru Pate, ya ce sun buɗe ofishin ne don kara hada kan dukkan ma’aikatan Telebijin da Radio a kasa Baki daya.

Haka zalika kungiyar ta bayar da kyautar na’ura Mai kwakwalwa guda daya don gudanar da aiyukan kungiyar a Sabon ofishin.

Pate, ya kara da cewa duk Wanda yake aikin Jarida Koda ya Yi ritaya yakamata ya shiga cikin kungiyar domin shima ya zama mamba.

Shugaban ya ce kungiyar tafi Mai da hankali wajen horas da mambonin ta da kuma kara mu su fasaha, sakamakon chanje-chanjen da Ake Samu a Radio da Telebijin, Inda sabbin fasahohi da kayan aiki suke fito wa, Wanda ya zama wajibi ma’aikatan kafafen yada Labaran su fahimci haka.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda