Gwamnatin Kano ta raba wa daliban firamare da sakandare kayan karatu
Gwamnatin Kano ta raba kayan koyo da koyarwa ga makarantun firamare da sakandire dake fadin jihar nan. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce samar da kayayyakin zai taimaka kwarai ga makarantun jihar nan domin farfaɗo da su. Kasancewar Inganta ilimi ne abin da Gwamnatinsa ta sa a gaba.