CBN ya janye dokar canjin dala kan shinkafa da wasu kayyaki 42

Babban Bankin Najeriya CBN ya ɗage haramcin bayar da canjin dala domin shigo da shinkafa da wasu kayyaki 42 cikin ƙasar nan a wani yunƙuri na tallafa wa kasuwar musayar kuɗi na ‘lokaci zuwa lokaci’.

A shekarar 2015 ne CBN ya taƙaita bayar da dala domin shigowa da wasu abubuwa ƙasar, yana mai cewa bai kamata a bayar da dala domin shigowa da su ba, kasancewar ana iya samar da su a cikin ƙasar.

To sai dai cikin wata sanarwar da CBN din ya fitar ranar Alhamis, mai ɗauke da sa hannun babban daraktan sadarwar babban bankin, Isa Abdulmumin, ya ce kayyakin da aka ɗage wa haramcin sun haɗa da shinkafa da siminti da man ja da nama da

Sanarwar ta ci gaba da cewa a yanzu masu shigo da abubuwa 43 za su iya samun chanjin dala daga babban bankin na CBN.

Post masu alaƙa

Wani raho bayyana yadda Malami ɗaya ke kula da ɗalibai 105 a makarantun gwamnatin Kano.

Hukuncin kotu kan jam’iyyar NDC koma baya ne ga dimokraɗiyya – PDP

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta kafa kwamitin da zai nemo hanyoyin da jami’anta za su mallaki gidaje.