Shugabannin Ƙungiyar Kano Leads sun kawo ziyara Muhasa

Shugabannin Ƙungiyar Kano Leads – Da Ruwana – sun kawo ziya gidan rediyon nan  da talabijin na Muhasa a yau Litinin, inda suka zo da buƙatun haɗa gwiwa a gudu tare a tsira tare.

Kano Leads Kungiya ce mai zaman kanta,  ta waɗanda suka damu da cigaban Kano da Kanawa, kuma masu fafutukar ganin sun kawo canji mai ɗorewa a fannoni da dama da suka haɗa da ilimi, da kiwon lafiya, da tattalin arziki, da tsaro, da muhalli, da cigaban al’umma, da kuma samar da ababen inganta rayuwa.

Galibin ƴan ƙungiyar sun yi ritaya bayan sun sadaukar da kai sun bauta wa ƙasa tuƙuru, amma duk da haka sun jajirce  wajen cigaba da taimaka wa al’ummarsu.

GA CIKAKKEN RAHOTON:

Post masu alaƙa

Gwamnan Kano ya naɗa Barista Hafsat Kutama shugabar hukumar PCACC

Rundunar yan sandan Kano ta kama mutane 10 da ake zargi da satar motoci tsakanin jihohi.

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa