Gwamnatin Kano ta raba wa daliban firamare da sakandare kayan karatu

Gwamnatin Kano ta raba kayan koyo da koyarwa ga makarantun firamare da sakandire dake fadin jihar nan. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce samar da kayayyakin zai taimaka kwarai ga makarantun jihar nan domin farfaɗo da su. Kasancewar Inganta ilimi ne abin da Gwamnatinsa ta sa a gaba.

Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a yayin bikin raba kayan, inda ya nemi waɗanda suka sami kayan karatun da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Daga bisani ya sa a kafa kwamiti don tantance malaman da suka ba da gudummawarsu wajen koyar da daliban jihar Kano cikin tsarin nan na  BESDA ya ce nan da mako biyu gwamnatin za ta sa su a sahun ma’aikatan jihar kano.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere