An kama Mai Satar Mutane Yayin Tantance Alhazai A Abuja
Hukumomin tsaro a Najeriya sun cafke wani kasurgumin dan ta’adda mai satar mutane ya karbi kudin fansa da aka jima ana nema ruwa a jallo a sansanin alhazai da ke Abuja.
Hukumomin tsaro a Najeriya sun cafke wani kasurgumin dan ta’adda mai satar mutane ya karbi kudin fansa da aka jima ana nema ruwa a jallo a sansanin alhazai da ke Abuja.
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci jama’ar sa su tashi da azumi gobe litinin da adduoi domin neman taimakon Allah.
Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ose ta jihar Ondo, Nelson Adepoyigi. Clement Kolapo Ojo, shugaban karamar hukumar Ose, ya tabbatar da mutuwar Adepoyigi a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Lahadi. Ojo, a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Oluwaseun Ogunniyi ya sanya wa hannu, […]
Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da Bikin “Kauyawa Day” a fadin jihar, tare da fitar da matakai guda shida da za su tabbatar da bin wannan doka da kuma cikar manufofin da aka sanya a gaba.
Kasar Burtaniya ta bayyana damuwarta kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, inda ta bayyana hakan a matsayin “babban abin tada hankali” da ke faruwa sakamon rikice-rikicen da suka ki ci-suka ki cinye wa a jamhuriya Nijar da kuma Kasar Sudan.
Wata Kotun Majistare da ke Jos a ranar Juma’a ta yanke wa wani ɗan kasuwa mai suna Shederack Danlami mai shekaru 22 hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bisa samunsa da laifin satar zakaru biyu.
Rahotanni da yammacin Laraba sun ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta tsare tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar wani yanki a jihar Jigawa, wato Honarul Muhammad Gudaji Kazaure bisa zargin shi da aikata laifukan kuɗi.
Wasu bankunan kasuwanci a Najeriya sun fara aiwatar da sabon ƙarin kuɗin tura saƙon SMS daga Naira 4 zuwa Naira 6.
Rahotanni daga jihohin Arewa Maso Gabashin Najeiya na cewa gwamnonin yankin na taro a Damaturu babban birnin Jihar Yobe kan matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Kungiyar Tuntuba Ta Arewacin Najeriya ACF ta bayyana cewa yankin Arewa zai mara wa ɗan takara baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ne kawai idan ya nuna ƙwarin guiwar kare muradun yankin.