ACF Ta Sanya Sharadi Ga Masu Neman Goyon Bayan Arewa A Zaben 2027

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Kungiyar Tuntuba Ta Arewacin Najeriya  ACF ta bayyana cewa sai ɗan takarar da ya nuna ƙwarin guiwar kare muradun yankin Arewa za ta mara wa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 .

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taro da kungiyar ta gudanar a Kaduna, inda aka tattauna kan manyan matsalolin da ke addabar Arewa da ma kasa baki ɗaya.

Alhaji Dalhatu, wanda kuma shi ne tsohon Ministan Lantarki da Karfe, ya jaddada cewa ACF ba za ta goyi bayan kowanne ɗan takara ko jam’iyya ba sai dai waɗanda suka nuna cikakken kishin yankin Arewa da niyyar magance matsalolinsa da suka hada da rashin tsaro, talauci da koma bayan tattalin arziki.

Ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta farka daga dogaro da alkawuran siyasa Mai kama da shificin gizo, tare da tabbatar da an zaɓi shugabanni masu gaskiya da rikon amana da za su kai yankin tudun mun tsira.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya