Mujahid Wada Guringawa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule Zata Karrama Aminu Dantata, Ahmad Bamba, Rabi’u Kwankwaso Da Wasu Fitattun Mutane

Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Jihar Kano, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya bayyana cewa jami’ar ta yanke shawarar karrama marigayi Sheikh Ahmad Bamba sakamakon gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jami’ar tun kafin rasuwarsa. Farfesa Kurawa ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai, inda ya ce wannan […]

Read more

Hisbah Ta Lalata Barasa Ta Naira Miliyan 5.8 A Jigawa

Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Ya ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin […]

Read more

Tinubu Zai Karɓo Rancen $21bn Daga Ketare

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta karɓo bashin ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatarwa da cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026. Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more […]

Read more

Ko Makiyan Buhari Sun San Bai Yi Sata Ba: Akpabio

Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya kwatanta marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na gari wanda ya mulki Najeriya ba tare da satar duƙiyar ƙasa ba. Akpabio, wanda ya bayyana haka a lokacin taron majalisar zartaswa da aka gudanar a Abuja don yi wa tsohon shugaban addu’o’i, ya ce masu sukarsa ma […]

Read more

Tinubu Ya sauya Sunan Jami’ar Maiduguri Zuwa Muhammadu Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari, marigayi shugaban Najeriya. Tinubu ya sanar da haka ne a taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. “Kafin mu fara addu’o’i domin karrama Buhari, ina sanar da ku cewa mun sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari,” in […]

Read more

Tinubu Zai Jagoranci Taron Yi Wa Buhari Addu’o’i A Abuja

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai jagoranci taron addu’o’i na musamman ga tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja, babban birnin ƙasar. Cikin wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labaran ƙasar ta fitar ta ce taron – wanda za a gudanar da misalin ƙarfe biyar na maraice agogon ƙasar – zai samu halartar ministocin gwamnatin ƙasar. Bayan […]

Read more