Mujahid Wada Guringawa

Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya amince da kafa kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa, wanda zai kasance ƙarƙashin jagorancin Kashim Ibrahim-Imam sai Nasir El-Rufai a matsayin mataimakinsa. Naɗin na zuwa ne yayin da El-Rufai ke tsare a hannun hukumomi bisa tuhume-tuhumen da gwamnati ke yi masa. Daraktan yaɗa labarai […]

Read more

Gwamnatin Nijar ta karɓi kashi 40 na aikin haƙar uranium

Gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta cimma yarjejeniya da kamfanin haƙar ma’adanai na Madaouela don sake fara aikin haƙar uranium, wani sabon mataki mai muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar. A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a Yamai ranar Laraba, gwamnatin Nijar ta karɓi kashi 40 na aikin haƙar uranium. Ana sa ran yarjejeniyar za […]

Read more

Kotu ta soke takarar gwamna da Pantami ke yi a Gombe

Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta rushe takarar Farfesa Isa Ali Pantami ɗantakarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, ta yanke hukuncin ne a wata ƙara da Usman Aliyu Garry ya shigar, inda yake ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna […]

Read more

Yara mata 4 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Yara mata huɗu sun riga mu gidan gaskiya a Jihar Jigawa, bayan kwale-kwalen ɗaukar fasinjoji ya kife a tsakiyar tafkin Dudduru, yayin da yake kan hanyarsa na zuwa kasuwa. Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, 2026, a tafkin da ke kusan kilomita uku daga ƙauyen […]

Read more