Gwamnatin Tarayya ta fitar da naira biliyan biyu da miliyan ɗari uku har da ɗoriya domin biyan bashin albashi da na ƙarin girma ga malamai a jami’o’in tarayya.
Wannan dai wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa jin daɗin ma’aikata da kuma ci gaba da tattaunawa da ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU.
Ministan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake jawabi kan tattaunawar da gwamnati ke yi da ƙungiyar ASUU da sauran ƙungiyoyin jami’o’i.
Ya ce an riga an tura kuɗin ta ofishin Akanta-Janar na Ƙasa (OAGF), kuma jami’o’in da abin ya shafa za su fara ganin saƙon biyan kuɗin a asusun su nan ba da daɗewa ba.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin kammala sakin kuɗaɗen da suka shafi fansho da sauran tsarabe-tsarabe na basussuka, sannan daga shekarar 2026, ƙarin kuɗin alawus na aikin koyarwa (Earned Academic Allowance – EAA) za a haɗa shi kai tsaye cikin albashin ma’aikata domin tabbatar da biyan kuɗaɗen yadda ya kamata.
- Gwamnatin Nijeriya Ta Karyata Zargin Yan Majalisar Amurka Kan Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla.
- Kano Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Shan Inna
Alausa ya tabbatar da cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar warware duk matsalolin da suka jima suna taƙaddama da ɓangaren ilimi, yana mai cewa duk tattaunawar da ake yi tana gudana ne cikin gaskiya da amincewa.
Sai dai ya jaddada cewa gwamnati za ta shiga yarjejeniyar da za ta iya ɗauka ne kawai la’akari da abin da tattalin arzikin ƙasa ya bayar da dama.
Ya ce kwamitin ƙarƙashin jagorancin Yayale Ahmed na ci gaba da zama tamkar wani tsani na haɗin kai tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin jami’o’i.
Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu wajen ganin an farfaɗo da harkokin ilimi a ƙasar nan