Wasu Yan Majalissar Wakilai Shida Sun Koma APC

Yanmajalisar wakilan Najeriya shida daga jihohin Enugu da Filato sun koma jam’iyyar APC mai mulki daga jam’iyyun adawa.

Matakin nasu ya sa jam’iyyar ta Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta samu rinjayen kashi biyu cikin uku a majalisar mai mambobi 360.

Biyar daga cikin ‘yanmajalisar na PDP ne daga jihar Enugua kudancin ƙasar, da kuma ɗaya na Labour Party daga jihar Filato a arewaci, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana.

Adadin mambobin APC sun kai 243 kenan, wanda ya zama 2 cikin 3 na mambobi 360. \

Rahoton ya bayyana mambobin babbar jam’iyyar adawa PDP sun koma 74, LP 21, NNPP 15, APGA 5, ADC 1, SDP 2, YPP 1.

Wannan cigaban da jam’iyar mai mulki ta samu zai iya ba ta damar sauya duk matakin da take so a majalisar yayin da tuni ‘yansiyasar Najeriya suka fara shrin babban zaɓe na 2027.

Post masu alaƙa

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi