An Sanar Da Kuɗin Aikin Hajji Na 2026 A Najeriya
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da farashin kujerar aikin Hajjin bana. Sabon farashin aikin Hajjin na shekarar 2026 miladiyya ya nuna cewa an samu ɗan ragi idan aka kwatanta da na 2025. Shugaban hukumar farfesa Abdullahi Saleh Usman, wanda ya sanar da hakan a wata hira da BBC daga birnin Makka na […]