• Home  
  • Ba mu ƙarƙare batun sauya kayan NYSC ba – Ministan Matasa
- Babban Labari

Ba mu ƙarƙare batun sauya kayan NYSC ba – Ministan Matasa

Ministan Raya Matasa na Najeriya, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta amince da sauya kayan masu yi wa ƙasa hidima na NYSC zuwa kayan Kampala ba. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ministan ya ce rahotannin da ke cewa an amince da amfani da Kampala a […]

Ministan Raya Matasa na Najeriya, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta amince da sauya kayan masu yi wa ƙasa hidima na NYSC zuwa kayan Kampala ba.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ministan ya ce rahotannin da ke cewa an amince da amfani da Kampala a maimakon kaki sun fassara kalamansa ba daidai ba, bayan wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels.

Ya ce lokacin hirar ya ambaci Adire da Ankara ne kawai a matsayin wasu daga cikin shawarwarin da ake tattaunawa a kan su, yana mai jaddada cewa har yanzu ba a yanke hukunci kan irin kayan ko tsarin da za a yi amfani da shi ba.

Ya ce, “Manufata ita ce in bayar da misalai na wasu daga cikin shawarwarin da aka gabatar yayin tattaunawa. Ban sanar da cewa an amince da wani irin kaya ya maye gurbin kakin NYSC na yanzu ba.”

Ministan ya ce duk wata matsaya da za a cimma za ta kasance ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da la’akari da abin da ya fi amfani ga shirin NYSC da kuma Najeriya baki ɗaya.

Mista Olawande ya ce “sauye-sauyen da ake shiryawa na da nufin inganta shirin ta hanyar ƙara wa matasa damar samun aikin yi, bunƙasa harkokin kasuwanci, ƙarfafa haɗin kan ƙasa, inganta ayyukan yi da kuma sauƙaƙa musu shiga rayuwar aiki bayan kammala karatu.”

Ya kuma ce “bai kamata muhawarar da ake yi kan kayan NYSC ta mamaye hankalin jama’a fiye da manyan sauye-sauyen da gwamnati ke shiryawa domin ƙarfafa matasan Najeriya da kuma bunƙasa ci gaban ƙasar.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000