Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da shirin tantance matakin ilimin ɗalibai a faɗin ƙasar nan domin duba yadda ɗalibai ke fahimtar abin da ake koya musu, tare da amfani da sakamako wajen tsara manufofi da shirye-shiryen bunƙasa ilimi.
Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad ce ta bayyana hakan yayin da ta kai ziyarar duba yadda ake gudanar da jarabawar tantance ilimi ta ƙasa a wasu makarantun da ke ƙaramar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.
Ta ce, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ware wannan mako a matsayin Makon Tantance Ilimi na Ƙasa, inda ake gudanar da tantancewar a matakan ilimin firamare da sakandare domin samun sahihin bayani kan matsayin ilimin ɗalibai.
A cewarta, ana gudanar da tantancewar ne ga ɗaliban aji biyar na firamare, aji biyu na ƙaramar sakandare (JS2) da kuma aji biyu na babbar sakandare (SS2), a zaɓaɓɓun makarantun gwamnati da masu zaman kansu a dukkan jihohin ƙasar.
Farfesa Suwaiba ta ce, ta zagaya makarantu uku, biyu daga cikinsu na sakandare, ɗaya kuma ta firamare, inda ta tabbatar da cewa an gudanar da jarabawar cikin tsari ba tare da wata matsala ba.
“Mun gano cewa, an fara jarabawar akan lokaci, ɗalibai kuma sun zauna yadda ya kamata bisa ƙa’idojin gudanar da jarabawa. Na gamsu da yadda ake gudanar da wannan aiki,” in ji ta.
Ta bayyana cewa, sakamakon tantancewar zai taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen gano matsayin ilimin ɗalibai da kuma tsara hanyoyin inganta koyarwa da ilmantarwa a makarantun ƙasar.
Ta kuma jaddada cewa, gwamnatin tarayya ta ba batun yaran da ba sa zuwa makaranta muhimmanci, tana mai cewa ana haɗa kai da hukumomi daban-daban domin dawo da su cikin tsarin karatun boko.
Ministar ta sanar da cewa, nan ba da jimawa ba za a fara wani shiri a Jihar Jigawa da zai mayar da aƙalla yara 5,000 da suka daina karatu ko kuma ba su taɓa shiga makaranta ba zuwa makarantu.
