Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kai ziyarar duba tsaro zuwa makarantar ƴan sanda ta Najeriya (POLAC) da ke Wudil, AIG Patrick A. Atayero inda ya gana da kwamandan makarantar domin nazarin matakan tsaro da ƙara inganta haɗin gwiwa.
Bayan haka, CP Bakori ya jagoranci sintiri a kan titin Kano–Maiduguri da iyakar Kano da Jigawa, a ƙarƙashin shirin Handshake Patrol, wanda babban sufeton ƴan sandan Najeriya ya ƙaddamar domin hana masu laifi zirga-zirga tsakanin jihohi.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa sintiri, tattara bayanan sirri da kuma gaggauta kai ɗauki domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ƙara da cewa sun tattauna kan yadda za a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin rundunar ƴan sandan Kano da kwalejin ƴan sandan, musamman wajen musayar bayanan sirri, ba da agajin gaggawa da kuma gudanar da aikin tsaro tare
Rundunar ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu ko mutum da ake zargi ga ofishin ƴan sanda mafi kusa ko ta layukan gaggawa na rundunar, 08032419754, 08123871555, 08076091271, 08028954037.

