Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaukacin yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na cikin duhu, da kuma wani yankin na Arewa ta Tsakiya. Mbah ta sanar da cewa manyan layukan wuta na 1 da na 2 da suka ƙarfin 330kv da suka tashi daga Ugwaji zuwa Apir, sun katse, inda har yanzu ake gudanar da binciken inda matsalar take.
A makonnin baya dai matsalar ɗaukewar wutar lantarki yana neman zama ruwan dare a Najeriya. Cikin watanni biyu, wannan shine karo na shida da babban layin raba hasken wutar lantarkin yana ɗaukewa.

