Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ce babu fashi dangane da gudanar zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe ranar Asabar mai zuwa.
Majalisar ta jaddada cewa babu abin da zai hana a gudanar da zaben ƙananan hukumomin kamar yadda aka tsara a ranar Asabar 26 ga watan Oktoba, 2024, duk da hukuncin Babbar Kotun Tarayya na soke Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC).
- Babban Layin Wutar Lantarkin Da Ke Kawo Wuta Arewa Ya Sake Ɗaukewa
- An Dakatar Da ‘Yan Jarida 14 Daga Ɗaukar Rahotanni A Gidan Gwamnatin Kano
A ranar Talata 22 ga Oktoba, 2024 ne dai mai shari’a Simon Amobeda na Babbar Kotun Tarayya ya ba da umarnin rushe shugabancin hukumar zaɓen jihar Kano, bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar na rashin cancantar shugabannin.
Mai Shari’a Simon Amobeda ya yanke hukunce-hukunce 10 dangane da hukumar zaben jihar Kano.