Babban Sufeton Yan Sandan Nijeriya Kayode Egbetokun Zai Ziyarci Jihar Kano

Rohatanni na cewa babban sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, zai kai wata Ziyara ta musamman jihar Kano, a ranar laraba 6 ga watan Agustan 2025.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayanin guraren da shugaban yan sandan zai ziyarta a jihar, amma dai ana saran zai gana da kwamishinan yan sandan Kano da kuma mataimakinsa dake kula da shiya ta daya dake Kano da kuma masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro.

Wannan ne karo na biyu da babban sufeton yan sandan Kayode Adeolu, ya zai ziyarci jihar tun bayan zuwansa a watan agustan shekarar 2023.

Post masu alaƙa

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP 

Kotun musulunci dake Jogana ta bayar da umarnin tsare mutanen da Ake tuhuma da yunkurin aikata tsafi.

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.