Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a zirin Gaza
Rundunar sojin Isra’ila ta fara samame ta kasa a kudancin zirin Gaza lamarin da ya jawo martini daga kasashen duniya.
Rundunar sojin Isra’ila ta fara samame ta kasa a kudancin zirin Gaza lamarin da ya jawo martini daga kasashen duniya.
Ana zargin shugaban hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON Farfesa Abdullahi Sale Pakistan da nuna bangaranci a hukumar wajen nada mukamai.
Rundunar Sojin Sudan ta bayyana cewa ta sake ƙwace iko da fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum a ranar Juma’a bayan gwabza yaƙi da rundunar RSF.
Rahotanni daga jihar Borno na cewa wadansu mutane da kawo lokacin rahoton nan ba a san ko su wanene ba sun kwashe kayan abincin wata motar Hukumar abinci ta duniya (WFP) a garin Gubio, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Damasak.
Tsohon gwamnan jihar kano kuma shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027 idan Allah ya kai mu.
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 20 ga watan Maris na kowacce shekara a matsayin ranar kula da lafiya da kuma tsaftar baki ta duniya. An fara ayyana ranar kula da lafiyar baki da hakora ne a shekarar 2007 amma ba a fara bikin ranar ba sai a shekarar 2013.. An ware ranar ce don […]
Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da dokar ta baci, da kuma dakatarwar da shugaba Tinubu ya yi wa gwamanan jihar Ribas Siminalayi Fubara cikin yanayi na kusan na bai daya.
Hukumar EFCC ta kama babban Akanta-janar na jihar Bauchi, Alhaji Sirajo Mohammed Jaja, kan zargin almundahanar naira biliyan 70.
Jaridar TRT Hausa ta bayyana cewa Gidan talbijin na Sudan ranar Alhamis ya ce sojojin ƙasar na dab da karɓe iko da Fadar shugaban ƙasar a Khartoum daga hannun dakarun rundunar RSF, lamarin da ya kawo wani babban sauyi a yaƙin da aka yi shekara biyu ana gwabzawa wanda yake barazanar raba ƙasar.
A ranar Talata ne, Shugaba Tinubu ya sanar da sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, inda ya bayyana cewa rikicin siyasar jihar yana barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya, inda mutane da dama ke ganin hakan bai dace da kundin tsarin mulki ba.
Ƙungiyoyin NLC da TUC sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta janye wannan mataki, don kada ya jefa Najeriya yanayin saɓa wa doka a nan gaba.