Mojtaba Khamenei ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa

Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa Ali Khamenei, wanda ya mutu a hare-haren Isra’ila da Amurka a ranar farko ta yaƙin.

A wani saƙo da aka wallafa da sunansa domin gode wa waɗanda suka halarci jana’izar mahaifinsa, Mojtaba Khamenei ya ce za su ɗauki fansar jininsa da kuma na sauran waɗanda suka mutu a harin da Amurka da Isra’ila suka kai wanda ya bayyana a matsayin kisan gilla.

Ya kuma jaddada cewa ɗaukar wannan fansa buri ne na al’ummar Iran, yana mai cewa dole ne a tabbatar an aiwatar da ita ba tare da gazawa ba.

Tun bayan da aka ce ya maye gurbin mahaifinsa a matsayin jagoran Iran, Mojtaba Khamenei bai bayyana a bainar jama’a ba, kuma har yanzu ba a ji saƙon murya ko na bidiyo daga gare shi ba, sai dai rubuce-rubucen da ake wallafawa da sunansa

Post masu alaƙa

Cutar Ebola ta kashe mutum fiye da 500 a Gabashin DR Congo

Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu – Iran