Labarai

Babban Labari Labarai

Gwamnati Ta Bai Wa ASUU N2.3bn Domin Biyan Bashin Albashin Malamai

Gwamnatin Tarayya ta fitar da naira biliyan biyu da miliyan ɗari uku har da ɗoriya domin biyan bashin albashi da na ƙarin girma ga malamai a jami’o’in tarayya. Wannan dai wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa jin daɗin ma’aikata da kuma ci gaba da tattaunawa da ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU. Ministan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, […]

Babban Labari Labarai

Gwamnatin Nijeriya Ta Karyata Zargin Yan Majalisar Amurka Kan Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla.

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan zargi ya ta’allaƙa ne da bayanai marasa tushe, waɗanda ba su san yanayin tsaron Najeriya ba. “Wasu daga cikin iƙirarin da jami’an Amurka suka yi […]

Babban Labari Labarai

Amurka Ta Soke Bizar Wole Soyinka

Fitaccen marubucin adabin nan ɗan Najeriya, Wole Soyinka, ya ce a bara Amurka ta dauki matakin kwace takardunsa na izinin shiga kasar. Mawalafin – wanda a shekarar 1986 ya lashe lambar yabo ta Nobel ɓangaren adabi – ya ce yanzu Amurkar ta soke takardun nasa domin haramta masa shiga ƙasar. Wole Soyinka ya ce Ofishin […]

Babban Labari Labarai

Majalissar Dattawan Nijeriya Zata Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro A Ranar Laraba

A gobe Laraba ne majalisar dattawa ta Najeriya za ta tantance sababbin manyan hafsoshin tsaron ƙasar da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa. Tinubu ya aike da sunayen sababbin hafsoshin ne zuwa ga majalisa domin tantancewa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada. Shugaban majalisar Sanata Godwill Akpabio ya tabbatar da karɓar wasiƙar ta shugaban […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000