Labarai

Babban Labari Labarai

Shu’aibu Abdulkadir Da Ake Tuhuma Da Halaka, Rumaisa Ya Musanta Zargin A Gaban Kotu.

Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Farida Rabi’u Danbaffa, ta ci gaba da sauraron shari’ar tuhumar da ake yi wa, Shu’aibu Abdulkadir da zargin kisan kan wata matar aure mai suna Rumaisa Shu’aibu. A zaman kotun na yau Alhamis, lauyan gwamnatin jihar Kano, Barista Basiru Kabiru Aliyu, ya roki kotun karkashin sashi na […]

Babban Labari Labarai

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Yi Nasarar Murkushe Harin Da Boko Haram Ta kai.

Rundunar sojin Najeriya ta ce masu iƙirarin jihadi sun ƙaddamar da hare-hare lokaci ɗaya kan sansanoninta huɗu da ke arewa maso gabashin ƙasar, sai dai ta samu nasarar murƙushe su. Sanarwar da rundunar haɗin gwiwa ta ‘Joint Task Force’ ta fitar a yau Alhamis, tare da sa hannun jami’in yaɗa labaran rundunar Laftanar Kanar Sani […]

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Babban Labari Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Umarnin Yin Bincike Kan Jerin Sunayen Masu Laifin Da Tinubu Ya Wa Afuwa

Babban ministan shari’a na Najeriya kuma babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, ya bayar da umarni ga hukumomi da dama su gudanar da bincike kan jerin sunayen masu laifin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi wa afuwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Hukumomin da za su gudanar da wannan binciken sun haɗa da hukumar […]

Babban Labari

NOA Ta Rushe Rundunar Yaki Da Rashin Da’a Ta War Against Indiscipline(WaI) Brigade

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta rushe rundunar sa kai ta War Against Indiscipline(WaI) Brigade, bayan amincewar majalisar zartarwa ta kasa, sannan ta maye gurbinta da Sabuwar Wata runduna mai suna Citizens Values Brigade. Bayanin hakan yana kunshe a cikin Wata sanarwa da Daraktan sadarwa da yada labarai, Bala Musa, ya rabawa […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000