• Home  
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Yi Nasarar Murkushe Harin Da Boko Haram Ta kai.
- Babban Labari - Labarai

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Yi Nasarar Murkushe Harin Da Boko Haram Ta kai.

Rundunar sojin Najeriya ta ce masu iƙirarin jihadi sun ƙaddamar da hare-hare lokaci ɗaya kan sansanoninta huɗu da ke arewa maso gabashin ƙasar, sai dai ta samu nasarar murƙushe su. Sanarwar da rundunar haɗin gwiwa ta ‘Joint Task Force’ ta fitar a yau Alhamis, tare da sa hannun jami’in yaɗa labaran rundunar Laftanar Kanar Sani […]

Rundunar sojin Najeriya ta ce masu iƙirarin jihadi sun ƙaddamar da hare-hare lokaci ɗaya kan sansanoninta huɗu da ke arewa maso gabashin ƙasar, sai dai ta samu nasarar murƙushe su.

Sanarwar da rundunar haɗin gwiwa ta ‘Joint Task Force’ ta fitar a yau Alhamis, tare da sa hannun jami’in yaɗa labaran rundunar Laftanar Kanar Sani Uba, ta ce mayaƙan sun dirar wa sansanonin ne ta hanyar buɗe wuta da ƙoƙarin cimma musu wuta.

Sanarwar ta ce “tsakanin tsakiyar dare zuwa ƙarfe huɗu na asuba, ƴan ta’adda sun ƙaddamar da wani shiryayyen farmaki kan dakarunta da ke Dikwa, da Mafa, da Gajibo da kuma Katarko a jihar Borno da kuma Yobe.

“A dukkanin hare-haren dakarun sun tsaya tsakin-daka, suka yi artabu cikin karsashi, suka murƙushe harin, inda suka yi wa ƴan ta’adda mummunar ɓarna”.

A lokacin wannan artabu, a cewar rundunar “martanin sojojin ya kai ga halaka ƴan ta’adda 50. Haka nan dakarun sun ƙwato bindigar AK-47 guda 38, da bindigar labarbar bakwai, da bindigar tarwatsa tankokin yaƙi guda biyar, da bindigar GPMG biyu da tarin gurneti da dubban harsasai.

“Bugu da ƙari dakarun Najeriya na ci gaba da neman sama da mutum 70 cikin waɗannan ƴan bindiga da aka raunata,” in ji sanarwar.

A ɓangare ɗaya “wasu daga cikin dakarun Najeriya sun samu rauni yayin artabun amma suna samun kulawa kuma ba sa cikin haɗari. Wasu motoci da kuma gine-gine sun ƙone sanadiyyar ruwan wuta daga jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai da ƴan ta’addan suka yi amfani da su da kuma wutar manyan bindigogi, musamman a Mafa da Dikwa,” kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Najeriya ta shafe sama da shekara 15 tana yaƙi da ƙungiyar Boko Haram wadda ke kai hare-hare kan jami’an tsaro da fararen hula a arewa maso gabashin ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa dubban rayuka da tarwatsa miliyoyi, tare da haifar da mummunar matsalar jin-ƙai.

Alƙaluman ƙungiyar ACLED mai sanya ido kan tsaro sun nuna cewa ya zuwa yanzu Boko Haram ta kai hari sau 333 a yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin wannan shekara.

Wani abu da masana tsaro ke nuna damuwa a kai shi ne yadda ƙungiyar ke amfani da fasahar zamani wajen kai hare-hare, kamar amfani da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai ko kuma wajen tattara bayanai.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai