• Home  
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Umarnin Yin Bincike Kan Jerin Sunayen Masu Laifin Da Tinubu Ya Wa Afuwa
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Umarnin Yin Bincike Kan Jerin Sunayen Masu Laifin Da Tinubu Ya Wa Afuwa

Babban ministan shari’a na Najeriya kuma babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, ya bayar da umarni ga hukumomi da dama su gudanar da bincike kan jerin sunayen masu laifin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi wa afuwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Hukumomin da za su gudanar da wannan binciken sun haɗa da hukumar […]

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Babban ministan shari’a na Najeriya kuma babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, ya bayar da umarni ga hukumomi da dama su gudanar da bincike kan jerin sunayen masu laifin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi wa afuwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hukumomin da za su gudanar da wannan binciken sun haɗa da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), da kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Ana hasashen cewa binciken zai iya kai ga cire fiye da rabin sunayen mutanen da aka yi wa afuwa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu dai na jira a mika masa jerin sunayen da aka tantance domin ya sanya hannu na karshe, a yunkurin tabbatar da cewa duk wanda zai amfana daga afuwar ya cancanta.

Tinubu dai ya yi amfani da ikon da ƙundin tsarin mulki ya ba shi wajen yi wa mutum 175 da aka samu da laifuka daban-daban afuwa.

Fagbem ne ya sanar da hakan a yayin taron Majalisar mahukunta da aka gudanar a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000