Labarai

Babban Labari Labarai

Gwamnan Abia ya ziyarci Tinubu a Villa

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ziyarci Shugaba Tinubu a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja. Duk da cewa babu cikakken bayani game da ziyarar, wasu a ƙasar na ganin ba ta rasa nasaba da batun shugaban ƙungiyar ƴan awaren Biafra, Nnamdi Kanu da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da rai cikin watan da ya […]

Babban Labari Labarai

Majalisar Dattawa ta yi sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta

Majalisar Dattawa ta sanar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta, musamman na tsaro da na tattara bayanan sirri sakamakon ƙalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga kwamitin zaɓe na Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio. A sabon tsarin, Sanata Yahaya Abdullahi […]

Babban Labari Labarai

Ministan Tsaron Nijeriya Ya Yi Murabus

Ministan tsaro na Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya ajiye aikinsa daga yau Litinin, 1 ga Disamba, 2025, bisa dalilan lafiya. Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta fitar ta ce Badaru ya sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu murabus ɗinsa a cikin wasiƙar da ya aika masa, inda ya ce ya yi hakan ne […]

Babban Labari Labarai

An Kama ’Yan Bindiga 4 A Kano

An kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne ɗauke da makamai da ake zaton bindigogi ne a tashar mota ta Ƙofar Ruwa da ke Jihar Kano. Tashar motar, wadda ke kusa da kasuwar kayan gini ta Ƙofar Ruwa a Ƙaramar Hukumar Dala. A cewar mazauna yankin, an kama mutanen ne lokacin da […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai