Labarai

Babban Labari Labarai

Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Umarnin Binciko Musabbin Mutuwar Kwamandan Yaki Da Kwacen Waya

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin ɗaukar mataki akan duk wanda aka samu da laifi kan sanadiyyar rasuwar kwamandan rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma daƙile shaye-shayen kayan maye ta Anti-Phone Snaching ta jihar Kano, Inuwa Salisu Sharaɗa. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin […]

Babban Labari Labarai

Wasu Yan Majalissar Wakilai Shida Sun Koma APC

Yanmajalisar wakilan Najeriya shida daga jihohin Enugu da Filato sun koma jam’iyyar APC mai mulki daga jam’iyyun adawa. Matakin nasu ya sa jam’iyyar ta Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta samu rinjayen kashi biyu cikin uku a majalisar mai mambobi 360. Biyar daga cikin ‘yanmajalisar na PDP ne daga jihar Enugua kudancin ƙasar, da kuma ɗaya […]

Babban Labari Labarai

Gwamnati Ta Bai Wa ASUU N2.3bn Domin Biyan Bashin Albashin Malamai

Gwamnatin Tarayya ta fitar da naira biliyan biyu da miliyan ɗari uku har da ɗoriya domin biyan bashin albashi da na ƙarin girma ga malamai a jami’o’in tarayya. Wannan dai wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa jin daɗin ma’aikata da kuma ci gaba da tattaunawa da ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU. Ministan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, […]

Babban Labari Labarai

Gwamnatin Nijeriya Ta Karyata Zargin Yan Majalisar Amurka Kan Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla.

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan zargi ya ta’allaƙa ne da bayanai marasa tushe, waɗanda ba su san yanayin tsaron Najeriya ba. “Wasu daga cikin iƙirarin da jami’an Amurka suka yi […]

Babban Labari Labarai

Amurka Ta Soke Bizar Wole Soyinka

Fitaccen marubucin adabin nan ɗan Najeriya, Wole Soyinka, ya ce a bara Amurka ta dauki matakin kwace takardunsa na izinin shiga kasar. Mawalafin – wanda a shekarar 1986 ya lashe lambar yabo ta Nobel ɓangaren adabi – ya ce yanzu Amurkar ta soke takardun nasa domin haramta masa shiga ƙasar. Wole Soyinka ya ce Ofishin […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000