Tinubu Ya Nemi Sabbin Hafsoshin Soja Su Daƙile Sabbin Barazanar Tsaro
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi sababbin hafsoshin tsaron ƙasar su zage damtse domin magance sababbin barazanar tsaro da ke kunnowa. Da yake magana bayan bikin ƙara wa shugabannin rundunonin soji girma yau Alhamis a Abuja, Tinubu ya ce: “Barazanar tsaro na ƙara sauyawa a kodayaushe, kuma abin da ya fi damun gwamnatinmu shi ne […]










