Ana zargin wata ɗaliba a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, da sa samarin ta su yi wa wani malaminsu mai suna Aliyu Hamza Abdullahi dukan kawo wuƙa.
A ranar Talata, 14 ga watan Janairu, 2025 ne haƙok budurwa ya cimma ruwa in da samarin ta suka samu nasarar yi wa malamin laga-laga.
Budurwar ta sa an yi wa Malamin, wanda shi ne jami’in jarabawar sashen karatu ta duka ne bayan ta zarge shi da ƙin sauya mata sashen abin da take karanta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne bayan da dalibar da ta nuna rashin gamsuwa da kwas din aka ba ta, ta buƙaci a canza mata amma sakamakon jarabawar ta bai kai na kwas ɗin da take so ba.
- Ya Kamata Sojoji Su Mamaye Dazukan Najeriya-Ganduje
- Ziyarar Muhasa Talabijin da Rediyo Zuwa Gidan Tarihi na jihar Maradi Dake Jamhuriyar Nijar.
Jami’in hulda da jama’a na kwalejin, Auwal Ismail Bagwai, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Bagwai ya ce, “Malamin ya samu raunuka a hannunsa yayin da yake kokarin kare kansa.
Ya tabbatar da cewa “Hukumomin tsaro suna bincike akan lamarin kuma a halin yanzu malamin da ya ji rauni yana samun kulawa a asibiti.”