Home » ‘Yan Ta’adda Na Shirin Kai Hare-hare A Kano

‘Yan Ta’adda Na Shirin Kai Hare-hare A Kano

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Gamayyar hukumomin tsaro a jihar Kano sun gargadi mutane da su kaucewa wuraren cunkoson jama’a sakamakon samun bayanan sirri kan yunkurin kawo hare-hare jihar da wasu yan ta’adda ke shirya wa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a ranar Juma’a.

Sanarwar ta yi kira da a kauracewa dukkan wuraren taruwar jama’a zuwa wani lokaci, don dakile wa da kuma bankado masu yunƙurin kawo hare-haren.

Sp Abdullahi Haruna ya ƙara da cewa don tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano, an yi duk shirin da yakamata na tsaro don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Haka zalika an baza jami’an tsaro na musamman waɗanda suka ƙware wajen ganowa da kuma daƙile aiyukan ‘yan ta’adda.

Rundunar ta shawararci al’umma a duk lokacin da suka ga wani abu da ba su gamsu da shi ba , su gaggauta sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa don ɗaukar matakinda ya dace.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?