Alh. Muhammad Babandede Ya Zama Jagora A Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai Ta Ƙasa
Alhaji Babandede wanda gogaggen ma’aikaci ne ya samu muƙamin ex-officio a IBAN domin kawo cigaba a harkokin kafafen yaɗa labarai a Najeriya.
Alhaji Babandede wanda gogaggen ma’aikaci ne ya samu muƙamin ex-officio a IBAN domin kawo cigaba a harkokin kafafen yaɗa labarai a Najeriya.
Masana kiwon lafiya a fannin ingantacen abinci wato dietians sun tabbatar da cewa rake na da muhimci ga lafiyar al’umma. Lokuta da dama mutane kan sha rake domin zaƙin da Allah ya hore masa ba tare da sanin alfanun da ruwan raken ke da shi ga lafiya ba. Masana kiwon lafiya sun gano cewa rake […]
Rahotanni dake fitowa daga jihar Sakoto na cewa masu riƙe da sarautun gargajiya aƙalla 19 ne suka yi murabus domin nuna goyon bayan su ga Sanata Ibrahim Lamido Waɗanda suka ajiye muƙaman nasu sun haɗa da Dagacin Sabon Birnin Gabas da Tsilba da Faru da Zumbuli da Dawakin da Kanwuri da Hande da Sabon Fegi […]
A ranar Litinin 28 ga Satumbar 2024 ake sa ran wa’adin da Ministan Abuja Nyesome Wike ya bai wa mabarata na su fice daga birnin zai ƙare. Kungiyar masu buƙata ta musamman dake Arewacin Najeriya ta yi kira ga ‘ya’yan ta da su tashi da azumi don neman taimakon Ubangiji bisa umarnin na ministan Abuja. […]
Sojojin ƙasar Isra’ila sun ce sun kai wasu hare-hare ta sama gabashin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Majalisar dattawan Najeriya ta ce tana da burin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar, ta yadda za’a samar da dokar da za ta hukunta iyayen da suka ƙi kai ‘ya ‘yansu makaranta . Shugaban kwamitin ilimi na majalisar dattawan, Sanata Lawan Adamu Usman ya ce majalisar na duba yiwuwar yin dokar ɗauri ta […]
Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya fasa zuwa taron da ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila ta Commonwealth na shekarar 2024, da za’a gudanar a tsibirin Samoa. Shettima ya fasa zuwa taron ne saboda matsalar da jirgin sa ya samu a lokacin da ya yada zango a ƙasar Amurka. Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo […]
Babban bankin kasa na CBN, ya yi watsi jita jitar da ke yawo cewa daga ranar 31 ga watan Disamban shekarar nan ta 2024, za’a daina amfani da tsofaffin takardun kudi Na Naira. Bayanin watsi da jita jitar na zuwa ne a jiya Alhamis, inda babban bankin ya bayyana magana a matsayin mara tushe […]
Tun bayan ɗaukewar babban layin wutar lantarkin da yake samar wa da Arewacin Najeriya wutar lantarki, iyalai da masana’antu a yankin suka shiga matsaloli saboda rashin hasken wutar. An sanar da cewa manyan layukan wuta na 1 da na 2 da suka ƙarfin 330kv da suka tashi daga Ugwaji zuwa Apir, sun katse, inda har […]
Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ce za ta ɗauki mataki a kan jihohin da suka ƙi gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ake sa ran zai tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomin kamar yadda kotun ƙolin ta zartar a kwanakin baya.