Abin Da Yasa Aka Ɗage “Quran Convention” A Najeriya 

Majalisar Ƙoli Ta Addinin Musulunci A Najeriya ta ɗage taron mahaddata Al-Qur’ani da ake yi wa laƙabi da Qur’anic Convention a Turance da za a gudanar a Abuja Saboda yawan waɗan da suka nuna sha’awar zuwa. 

Bayanin ɗage taron na ƙunshe a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar a yammacin ranar Asabar 15 ga Fabarairun 2025.

Sanarwar ta ce, kwamitin shirya taron ya tsara karɓar mahaddata dubu 30 ne, amma yanzu haka sama da mutane dubu ɗari biyar sun bayyana sha’awar halartar taron.

A takardar sanarwar ɗage taron, an bayyana cewa, an samu dubban mutane daga ƙasashen ƙetare da suka bayyana sha’awar halartar taron, abin da ya wajabta wa majalisar neman kwamitin ya ɗage taron.

Majalisar ta nemi kwamitin shirya taron mahaddata Al-Qur’anin ya sake shiri na musamman domin karɓar masu niyyar zuwa taron.

Post masu alaƙa

Masu Garkuwa Da Janar Rabe Na Neman A Sako ’Yan Bindigar Da Ke Hannun Gwamnati

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano