Tirela Ta Yi Ajalin Mutane 23

Wasu mutane 23 sun gamu da ajalinsu a wani hatsari da ya rutsa da su a gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke hotoro kan hanyar Kano zuwa Maiduguri a ranar Juma’ar da ta gabata.

Hukumar FRSC ta ce, hatsarin ya faru ne sanadiyyar wata tirela ɗauke da mutane da kayayyaki.

Binciken farko da hukumomi suka gudanar ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon tukin ganganci wanda aka fi alakƙanta shi da faruwar lamarin.

Hatsarin ya rutsa da a ƙalla mutane 71, inda 48 suka samu raunuka, yayin da 23 suka mutu.

An ce jami’an bayar da agajin gaggawa na FRSC tare da haɗin gwuiwa da rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun isa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa domin kai agaji ga waɗanda abin ya rutsa da su.

Post masu alaƙa

Masu Garkuwa Da Janar Rabe Na Neman A Sako ’Yan Bindigar Da Ke Hannun Gwamnati

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano