Shugaba Tinubu Ya Ciwo Bashin Tiriliyan 50 Kawo Yanzu
A watanni 19 na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a mulkin Najeriya, ƙididdiga ta tabbatar da cewa gwamnatinsa ta ciyo bashin da ya haura Naira tiriliyan 50, wanda ya zarce rabin wanda ta gada.
A watanni 19 na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a mulkin Najeriya, ƙididdiga ta tabbatar da cewa gwamnatinsa ta ciyo bashin da ya haura Naira tiriliyan 50, wanda ya zarce rabin wanda ta gada.
Jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens sun aika mayaƙan Boko Haram kimanin 50 barzahu yayin musayar wuta a Jihar Kaduna.
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya musanta zargin da ke cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohinsu.
Kwalara na daya daga cikin ƙwayoyin cututtuka da suke yaduwa ta hanyar ruwa, ko ta abinci maras tsafta. Kwalara na haifar da amai da gudawa, kuma tana saurin yin kisa idan har ba a ɗauki mataki a kan lokaci ba. Waɗanda cutar ta yi wa tsanani za su yi fama da rashin ruwan jiki wanda […]
A wata sanarwa da majalsair malaman addinin Musulunci ta Najeriya ta fitar a ranar Litinin 18 ga Nuwamba, 2024, ta bukaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da kudurin yi wa dokar haraji gyaran fuska.
‘Yan Majalisar Wakilai da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna damuwarsu kan wasu kudurori hudu da zasu sake fasalin dokar harajin Najeriya.
Dan Tiktok Emmanuel Nabugodi ya bayyana ne a gaban kotu a ranar litinin, bayan ya amsa laifinsa a makon da ya gabata kan wasu tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da wasu kalamai na nuna ƙiyayya da yaɗa munanan bayanai game da shugaban ƙasa Yoweri Museveni.
Majalisar dinkin duniya ta ce an sace abincin agaji da ke cikin motoci kusan 100 da za a kai wa Falasɗinawa ranar 16 ga watan Nuwamba a wani mataki da ake gani yana cikin sata mafi muni a watanni 13 da aka kwashe ana yaƙi a yankin.
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Afirka ta ayyana ƙyandar biri a matsayin cuta mai matuƙar haɗari, bayan ɓullar sabon nau’in cutar da ke yaɗuwa cikin sauri. Cutar na ƙara yaɗuwa cikin sauri a bana, tun bayan da aka fara samun wanda ya kamu da ita a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo. Tun daga farkon shekarar […]
‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce akwai shiri mai karfi na yi wa Arewacin Najeriya mulkin mallaka daga jihar Legas.