Tsohon gwamnan Kaduna ya gargadi ECOWAS kan afkawa Nijar da yaki
Nasiru El-Rufai ya kasance na kusa da shugaban kasa, Bola Tinubu inda ya shawarce shi kan matakin soji da kungiyar ECOWAS ke son dauka kan Jamhuriyar Nijar
Nasiru El-Rufai ya kasance na kusa da shugaban kasa, Bola Tinubu inda ya shawarce shi kan matakin soji da kungiyar ECOWAS ke son dauka kan Jamhuriyar Nijar
Matan da ke gabatar da shirin ‘Mata A Yau’ a wani gidan talabijin a nan Kano, sun ziyarci shugaban hukumar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan wasu kalaman da suka yi, a cikin shirin dangane da batun gaisuwa tsakanin mata da miji.
Sabuwar ministar ma’aikatar yawon bude ido, Misis Lola Ade-John, ta ce za ta yi aiki tare da ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki don mayar da bangaren yawon bude ido ya zama babban hanyar samun kudaden shiga ga Nijeriya.
A wani labarin kuma sababbin ministocin tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, suna shan suka da caccaka daga ƴan Najeriya saboda rashin gogewar aiki a ɓangaren da aka ba su.
A wani yunkurin gwamnatin kasar nan na bunkasa amfani da Gas a matsayin makamashin da motoci za su yi aiki da shi, Shugaba Bola Tinubu ya amince da wani shirin gwamnatin tarayya don cimma wannan manufa.
Mataimakiyar shugaban kula al’amuran daliban wata jami’a mai zaman kanta a kano ta bayyana cewa jami’ar na shirin zakulo hazikan dalibai ‘yan asalin Jihar
Daruruwan mata musulmai a nan jahar Kano sun gudanar da gangamin Taron Addu’a da nufin neman sassaucin matsin rayuwa da al’uma suke ciki.
Manyan hafsoshin tsaron ECOWAS za su sake yin wata ganawa ta musamman a kasar Ghana don ci gaba da tattauna yiwuwar amfani da karfin soja, a kan sojojin Nijar, musamman a yanzu da suke barzanar hallaka hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEAreshen jihar Kano ta yi nasarar kama wata allura mai bugarwa, wadda nauyinta ya kai kilogiram 2,000 tare da kama wasu mutane biyu.
Gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da Gwamnan Babban Bankin ƙasar nan, Godwin Emefiele da wasu ƙarin mutanan da aka dakatar da su a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis mai zuwa bisa zargin almundahanar Naira biliyan 6.9.