An fara caccakar sabbin ministocin tsaro daga Arewa

A wani labarin kuma sababbin ministocin tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, suna shan suka da caccaka daga ƴan Najeriya saboda rashin gogewar aiki a ɓangaren da aka ba su.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum  sun ce naɗa su a matsayin manyan masu jagorantar harkar tsaro a Najeriya, na cikin abubuwa mafiya ba-zata da ban mamaki da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Babban ministan tsaron, Muhammad Badaru Abubakar, ya buɗi ido ne a fagen kasuwanci da masana’antu, kafin ya faɗa siyasa. Shi ma, BelloMatawalle bai sai komai kan harkar tsaro ba, tsohon malamin makaranta ne.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa

Jami’ar Azare Za Ta Bai Wa Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Digirin Girmamawa