Tallafi ya kamata a ba wa daliban Jami’a ba bashi ba ~ Shugaban ASUU
Shugaban ƙungiyar malaman jami’a, ASUU, farfesa Emmanuel Osodeke, Ya ce matuƙar gwamnatin tarayya ta gaza dakatar da yuwuwar cigaba da ƙaruwar kuɗin makaranta ba a jami’o’in ƙasar nan, akwai yuwuwar kaso 40 zuwa 50 na ɗalibai za su gaza cigaba da karatu daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.