Gobara ta Tashi a Kotun Ƙolin Najeriya

A cigaba da kawo muku labari game da gobarar da ta tashi a kotun ƙolin Najeriya da ke Abuja a yau.

Shugaban Hukumar agajin gaggawa a Babban Birnin Tarayya, Abbas Idris, ne ya tabbatar wa da majiyarmu da faruwar lamarin, inda ya ce tuni jami’an kai ɗauki suka isa harabar kotun.

Sai dai ya tabbatar da cewa wutar ta shafi wani ɓangare ne kawai na kotun.

A cewarsa: ofisoshi biyu ne lamarin ya shafa kuma babu wanda ya rasa ransa a yayin gobarar.

Ya ƙara da cewa yanzu haka jami’an kai ɗauki sun samu nasarar shawo kan wutar.

Bayanan farko-farko da ke fitowa dai sun nuna cewa wutar lantarki ne ya haddasa gobarar.

Post masu alaƙa

Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.