Gwamnatin Zamfara za ta dau mummunan mataki kan masu satar ma’adanai

Gwamnan jihar Zamfara, Sauda Lawal Dare, ya umarci jami’an tsaro da su ɗauki tsattsauran mataki kan masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan umarni ya fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris wanda ya ce yaƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba na daga cikin dalilan da suke cigaba da haɓaka ayyukan ‘yan bindiga da ma sauran ayyukan ta’addanci a jihar.

A cewarsa, lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a jihar domin samar da zaman lafiya ga al’ummar jihar.

Wannan ta sa gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su harbe nan take duk wani wanda aka samu yana haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.  

Ya ce wannan mataki ya zama wajibi domin gwamnatin jihar ta gaggauta samar da cikakken ikonta a kan ma’adanan da ke jihar da kuma kiyaye lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar.

Post masu alaƙa

Babandede Ya Ziyarci Iyalan Hon. Laushi, Ya Ba Su Tallafi

Da Fulani Aka Kama da Wuraren ƙera Makamai a Filato, da War Haka Duniya ta Dauka:-Zagazola Makama

Gwamna Bala Mohammed ya canja sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APM