Shugaban Kasar Najeriya Ya Amince da Nadin Hafsoshin Sojin Kasar da Mashawarci Kan Tsaro
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da yi wa dukkan hafsoshin tsaron Nijeriya da sufeto-Janar na ‘yan sanda da masu ba da shawara kan sha’anin tsaro da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam murabus daga Ma’aikatunsu tare da maye gurbinsu nan take.