Angola: ‘Yan sanda sun tarwatsa mutanen dake zanga-zanga kan karin farashin man fetur

‘Yan sanda a Angola sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun mutanen da suka fito suna zanga-zanga kan karin farashin man fetur a ƙasar.

Dubban mutane sun fantsama kan tittuna a birnin Luanda da sauran manyan birane.

Angola da ke ta biyu a arzikin man fetur a Afirka – ta zabtare kuɗin tallafin da take bayarwa a fetur a watan da ya gabata, lamarin da ya ninka farashin a gidajen mai.

‘Yan adawa da ƙungiyoyin fararan-hula sun ce an yi gaggawa wajen cire tallafin, tare da kira ga ‘yan sanda su daina amfani da ƙarfi kan masu bore.

A makon da ya gabata mutum biyar aka kashe lokacin da ‘yan sanda suka buɗe wuta kan direbobin tasi da babura da ke zanga-zanga.

Post masu alaƙa

Manjo Janar Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Yan Bindiga

JIBWIS Gwallaga Sun Ziyarci A Sansanin Alhazai Na Jihar Bauchi Domin Bada Agaji

‘Yan Arewa A Jihohin Kudu Sun Koka kan Tsangwama da Wariya Saboda Matsalolin Tsaro