PDP ta kafa kwamatocin riƙo a jihohin Enugu, Delta, Rivers
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce ta kafa kwamatoci na riƙon ƙwarya da za su kula da shugaancin jam’iyyar a jihohin Enugu da Delta da Rivers – dukkansu a kudancin ƙasar. Wata sanarwa da ta fitar a yammacin yau Juma’a, PDP ta ce kwamatin gudanarwa ne ya amince da kwamatocin riƙon bisa […]