Tsohon Shugaban Hukumar Shigi da Fici ta Najeriya, Muhammad Babandede, OFR, OCM, ya sabunta rajistar zamansa ɗan jam’iyyar APC a Hadejia, Jihar Jigawa.
Babandede ya samu gagarumar tarba daga dimbin magoya baya da suka tarbe shi, daga ƙofar gari har zuwa mazabarsa ta Kasuwar Ƙuda, tafiyar mintuna kaɗan ce, amma ta ɗauki sama da awa huɗu saboda yawan jama’ar da suka fito.
Muhammad Babandede ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Ɗanmodi, tare da tabbatar da goyon bayansa ga jam’iyyar APC.
Dattijo kuma gogaggen ɗan siyasa Ambasada Haruna Ginsau, da Shugabannin jam’iyyar APC sun yaba masa kan biyayya da sadaukarwa ga jam’iyya.
Abin da aka tsara ya ɗauki yan mintuna amma ya ɗauki sama da awa huɗu saboda yawan jama’a daga sassa daban-daban na Jihar Jigawa, musamman mazaɓar sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas.