Ma’aikatar Lafiyar Najeriya ta bayar da umarnin sallamar duka daraktocin da suka shafe shekaru takwas a muƙamansu, nan take.
Wannan mataki na zuwa ne bisa ga manufofin wa’adin shekaru takwas da dokokin sabunta aikin gwamnati suka tanada, inda ake buƙatar daraktoci su yi ritaya bayan cikar wa’adin.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar “ta umurci shugabannin hukumomi su tabbatar an sallami duk wanda ya cika wannan wa’adin daga 31 ga Disamba, 2025.”
Haka kuma an buƙaci “karɓar takardu da kadarorin gwamnati daga hannun ma’aikatan da abin ya shafa.”
Ma’aikatar ta kuma umarci “sassan da abin ya shafa su dakatar da albashin daraktocin daga sashen IPPIS, sannan su tilasta musu mayar da duka alawus da aka biya bayan ranar da ya kamata su bar aiki.”
Wannan mataki ya sake jaddada wata sanarwa ta baya daga ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya wadda aka fitar a ranar 10 ga Fabrairu, 2026.
Hukumomin ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati da ma’aikatar za su gudanar da bincike don tabbatar da aiwatar da wannan umarni, inda rashin bin umarnin zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Ma’aikatar ta yi kira ga dukkan shugabanni su ɗauki wannan mataki da muhimmanci domin kiyaye tsari da doka.