Majalisa Za Ta Yi Zaman Gaggawa Saboda Zanga-zanga
Majalisar wakilan Najeriya za ta yi zaman gaggawa ranar Laraba, 31 ga Yuli, 2024 domin shawo kan masu zanga-zanga.
Majalisar wakilan Najeriya za ta yi zaman gaggawa ranar Laraba, 31 ga Yuli, 2024 domin shawo kan masu zanga-zanga.
Shugabannin jam’iyyar APC a jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja, sun ce ba za su naɗe hannu suna gani a kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da sunan zanga-zanga ba. Da yake yi wa manema labarai jawabi a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar Litinin a Abuja, shugaban jamiyyar […]
Masu zanga-zangar sun fantsama kan manyan titunan jihar, ciki har da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A cikin wani sabon faifan bidiyon da Bello Turji ya sake fitarwa, ya ce Matawalle na da hannu wajen tallafawa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Tsohon ɗan majalisar tarayya kuma jigo a siyasar Arewa, Dokta Usman Bugaje ya bayyana cewa ‘yan Najeriya su fito suyi zanga zanga, domin nuna bacin ransu ga halin matsi da suke ciki. Bugaje ya nuna takaicin sa kan yadda gwamnatin ke wadaka da kuɗi wajen gina gidaje da kuma siya wa shugaban ƙasa jirgin sama, […]
Gwamnatin Najeriya ta dauki matakan tsaurara tsaro a iyakokin kasar gabanin zanga-zanga da ake shirin farawa ranar Alhamis ga watan Agusta, 2024.
Wasu Mata magoya bayan Sanata Muhammad Ali Ndume sun yi barazanar yin zanga-zanga tsirara a Majalisar Dokoki ta Kasa, idan ba a mayar da shi kan shugabancin kwamitocin Majalisar Dattawa ba. Magoya bayan sanatan sun yi wannan barazana ne a lokacin da Ndume ya karbi bakuncinsu tare da sauran magoya bayansa a gidansa da ke […]
Sakataren Kungiyar Fafutikar Sake Farfaɗo da Arewa Dokta Salisu Nani Zigau, ya ce suna goyon bayan shirin zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a Najeriya.Da ya ke magana da yawun ƙungiyar, ya ce suna da yakinin cewa matakin wannan zanga-zanga da ke tafe zai kawo sauyin da ake matukar buƙata a Najeriya a halin yanzu. Jaridar […]
Karamin sashe na ɗaya na babban sashe na huɗu na dokar albashin Najeriya na 2019 da aka yi wa kwaskarima a 2024 ya ce biyan albashi mafi ƙaranci na naira dubu 70 bai shafi wasu ma’aikatu ba. Sashen ya lissafo su kamar haka: Ma’aikatun da ke da ma’aikatan wucin-gadi. Dillalai, waɗanda ma’aikatu ke biyan su […]
Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta bukaci matasa su nisanci zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a fadin kasar.