Al’ummar yankin ƙaramar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna na zargin jiragen sojin saman Najeriya da jefa musu bom a masallaci da kuma kasuwa wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23.
Sai dai a nata ɓangaren rundunar sojin sama ta Najeriya ta musanta wannan zargi, ta kuma bayyana cewa harin da ta kai ya tafi kai tsaye ne sansanin babban ɗan dindiga mai suna Kadaɗe Gurgu, wanda na hannun daman ɗan ta’adda Dogo Giɗe ne.
A nasu ɓangaren mazauna ƙauyen Jika da Kolo da ke yankin Yadin Kidandan sun shaida wa mane ma labarai cewa akwai mutanen cikin wanda harin da sojin su ka kai ya shafa.
- Gwamnatin Tarayya Ta Raba Motoci Guda 64 Masu Amfani Da Iskar Gas
- Kashi 40 Na Ƴan Najeriya Na Samun wutar Lantarki Na Awa 20 A kullum – Gwamnati
Mutenen garin sun kamanta harin da sojin suka kai da wanda aka kai a baya wanda yayi sanadiyyar rasa ran ƴan Mauludi kimamnin guda 100, a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar Hukumar Igabi a watan Disamban 2023.
Zuwa yanzu dai rundunar sojin ta Njeriya ta kafe akan cewa ba ta kai harin ba, kuma duk wani bayani zai zo ne bayan ta kammala bincike. Rundunar ta ƙara da cewa ta kashe yan ta’adda da dama yayin harin da ta kai, amma babu masallaci a wurin da jiragen suka kai harin.
Wasu Majiyoyi sun tabbatar da cewa anyi jana’izar mutane da suka rasu su 23 .